Northern States Civil Society Networks seeks Collaboration with EFCCHausa Translation:Kungiyoyin Arewacin Najeriya Sun Bukac…

Northern States Civil Society Networks seeks Collaboration with EFCC

Hausa Translation:

Kungiyoyin Arewacin Najeriya Sun Bukaci Hadin Gwuiwa Da Hukumar EFCC

Wata hadakar kungiyoyin cigaban yankin arewacin Najeriya CNSCSN, ranar Alhamis, 3 ga watan Maris, 2022 ta bukaci hadin gwuiwa da hukumar EFCC a yaki da cin hanci da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa da ma nunawa kungiyoyin amfanin bin dokar yaki da safarar kudin haram. Ta SCUML/
Shugaban hadakar kungiyar, Ibrahim Waiya ya bayyana bukatar hadin gwuiwar lokacin da suka kawo ziyara hedikwatar EFCC dake Jabi Abuja.
Ya bayyana cewa a shirye suke su taimakawa hukumar EFCC wajen wayar da kan al’umma da sauran masu ruwa da tsaki a kan ayyukan EFCC da tabbatar da dokokin ta da sauran hanyoyin da za su taimaka wajen bin dokar hana safarar kudin haram,
Har wa yau, shugaban hadakar ya yabawa shugaban EFCC saboda nasarorin da ya samu shekara daya da ya yi inda yay aba irin tsarin shugabancin Shugaban EFCC.

Shugaban hukumar EFCC Abdurasheed Bawa ya mika godiyarsa ga hadakar kungiyoyin saboda ziyarar da suka kawo.
Ya ce bukatar hadin gwuiwar ya yi daidai da wasu muradun hukumar EFCC biyu da suka hada da wayar da kan al’umma da hadin gwuiwa tare da masu ruwa da tsaki inda ya umarci sashen hullda da jama’a wajen tabbatar cewa an yi tafiya tare da kungiyoyin wajen cimma na wayar da kai.

Kuy ziyarci sashen intanet na EFCC a www.efccnigeria.org don karanta karashen labarin.

Share on Facebook «||» Share on Twitter «||» Share on Reddit «||» Share on LinkedIn