Alleged N761.6m Oil Fraud: Bawa’s Cross-examination Ends As Court Adjourns Nadabo Energy Boss’ Trial Till May 10
Hausa Translation:
Zambar Mai Ta N761.6m: An Kamalla Sauraren Kalubalantar Shaidar Da Shugaban EFCC Bawa Ya Yi
Ranar Litinin 9 gawatan Mayu aka ci gaba dasauraren karar da ake wa Abubakar Ali Peters da kamfaninshi Nadabo Energy Limited, a gaban mai shari’a S.S. Ogunsanya dake kotun jihar Legas a Ikeja
EFCC na tuhumar Ali akan laifuka masu alaka da zambar rarar mai ta kudi nera miliyan dari bakwai da sittin da daya.
Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya kammala amsa tambayoyi daga lauyan dake kare wanda ake tuhuma inda ya kalubalanci shaidar da shugaban EFCC ya bayar.
Bawa ya fadawa kotu cewa wanda ake tuhuma ya rubuta musu cewa a shirye yake ya biya gwamnati kudin da ya yi rara.
An daga sauraren karar zuwa 10 ga watan Mayu,2022.